Mutane da dama suna son zama masana na'ura (computer) da kuma zama kwararru a fannin, amma saboda rashin sanin makamar aikin ta inda zasu fara koyon fannin ilimin computer ya sa na dauki aniyar yin dan wannan rubutu domin fayyace masu wasu takakai kamar haka da zasu kai su zuwa ga zama kwararru a fannin computer:
1. Computer Literacy― Abu na farko shi ne ka san ita kanta computer din mece ce ita (computer Basics), da yadda ake amfani da ita da sarrafata (computer operation) da abun da ya hada da Microsoft Office (Words, Excel, Presentation, Access). Sannan kuma a wannan matakin ne zaka san yadda ake amfani da shortcuts keys na computer, da yadda ake warware wadansu 'yan kananun matsalolinta. Duk wanda ya iya wannan shi ake kira ‘Computer literate’
2. Computer Programming ― Bayan ka san yadda ake amfani da computer - to a wannan matakin ne zaka san tsare-tsaren computer, da yadda ake shirya ma ta umarni (dokoki da ka'idoji) domin ta aikata wani aiki kamar samar da fasahohin zamani irinsu: manhaja (software), shafin yanar-gizo (website), machine learning, wasan na'ura (game), da sauransu. Duk wanda ya iya wannan shi ake kira ‘Computer programmer’.
3. Computer Engineering ― Mataki na karshe shi ne ka san zahirin fasahar na'ura (computer), da yadda ake kirkirarta, gyarata, ingantata (domin ta yi daidai da zamani). Duk wanda ya iya wannan shi ake ‘Computer engineer’
Duk wanda ya zo wannan mataki na karshe kuma ya karance shi - to shi ne ya san ciki da wajen na'ura mai kwakwalwa (computer), kuma za'a iya kiransa da kwararren masanin na'ura.
Allah ya bamu ilimi mai albarka!
© Haruna Abdussalam
03/10/2022